Yajin Aikin NARD: Ministan Kwadago ya Bayyana Dokar da Zai Dauka Kan Likitoci

 

Ministan kwadago Chris Ngige, ya ce ya ja kunnen ‘ya’yansa likitoci da kada su shiga yajin aikin nan na rashin hankali.

Ngige ya bayyana cewa ba zai cigaba da sasanci da likitoci ba, zai dauka matakin hana su albashi idan har basu koma aiki ba.

Ministan yace ya gana dasu har sau biyu, don haka yana da wasu ayyuka a gabansa, ba zai cigaba da bata lokacinsa ba.

FCT, Abuja – Chris Ngige, ministan kwadago na Najeriya yace ya ja kunnen ‘ya’yansa likitoci da kada su kuskura su shiga wannan yajin aikin da ake yi wanda ya kwatanta da “rashin hankali”.

Kokarin da gwamnatin take yi na ganin cewa likitocin sun janye yajin aikin da suka fada ya gagara.

Wanne mataki gwamnatin tarayya za ta dauka?

Amma yayin magana da Channels TV shirin siyasarmu a yau na daren Juma’a, Ngige ya ce yana da ‘ya da ‘da da suke likitoci ne a kasar nan.

Ministan ya sha alwashin amfani da karfin iko kan likitcoin idan suka cigaba da wannan yajin aikin. Ya ce in har suka ki komawa bakin aiki nan da mako na gaba, zai saka dokar babu biya.

A mako mai zuwa zan tada wannan al’amarin saboda sasanci ya ki aiki.

Ba zan sake ganawa dasu ba saboda ina da abubuwan yi. Sasanci biyu nayi jiya, zan cigaba da bata lokacina a kansu ne?

Ina da wasu mafita a cikin dokokin kwadago kuma zan yi amfani dasu. Zan yi amfani da sashi na 43. Na sanar da NARD ba zasu samu albashi ba a yayin da suke yajin aiki kuma ba zai taba shiga cikin tarinsu na fansho ba.

Ko a dokokin kwadago na duniya, an goyi bayan hakan saboda suna tsayar mana da ayyukan da suka zama dole. Bai dace su shiga yajin aiki ba ba tare da sun sanar damu ba ana sauran kwanaki 15.

Abubuwa zasu sauya nan da mako mai zuwa. Su jira su gani, gwamnati suke so gwadawa. Suna wasa da rayuka. Na ja kunnen ‘ya’yana likitoci da kada su shiga yajin aikin rashin hankalin nan.

Ya gwamnatin tarayya zata yi idan babu likitoci?

A yayin da aka tambaye shi ko gwamnatin tarayya zata iya al’amura babu likitoci balle a yanzu da aka samu barkewar korona da amai da gudawa, Ngige yace sun shawo kan komai.

Ya kara da dora laifi kan gwamnatocin jaha inda yace jama’a suna magana kan gwamnatin tarayya ne kadai ba tare da sun duba na jahohi ba.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here