‘Yan Najeriya Sun Mayarwa da IBB Martani Kan Batun Cewa Mulkinsa ya yi Yaki da Rashawa Fiye da Mulkin Buhari

 

Cece-kuce sun barke bayan tsohon shugaban kasa Janar Ibrahim Babangida yace mulkinsa ya yi yaki da rashawa fiye da mulkin Muhammadu Buhari.

IBB ya tunatar da lokacin da ya sauke gwamna kan ya saci N313,000 amma kuma a yau masu mulki suna satar biliyoyi kuma suna tafe hankali kwance.

Wadannan maganganun nashi sun janyo surutai iri-iri har wasu suke bin bayansa yayin da wasu kuma suka ki amincewa da wannan batun nashi.

Minna, Niger – Cece-kuce ya barke tun bayan wani tattaunawa da aka yi da tsohon shugaban kasa na mulkin soji a ARISE TV inda yace mulkinsa ya yi yaki da cin hanci da rashawa fiye da mulkin shugaba Muhammadu Buhari.

IBB ya tunatar da yadda ya sauke gwamna akan satar N313,000 amma a halin yanzu mutane da dama da suka saci biliyoyin nairori suna yawonsu a cikin kasar nan.

Wannan furucin nashi ya janyo cece-kuce, wasu suna sukar maganarsa yayin da wasu suka amince da maganarsa inda suke cewa rashawa tana kara yawaita a Najeriya.

Ga wasu daga cikin martanin jama’a Daily Trust ta tattaro wasu daga cikin tsokacin jama’a.

Misali daya daga cikin masu tsokaci ya zargi IBB da zama tushen rashawa a Najeriya.

A tarihi, IBB shine ya halasta rashawa a Najeriya,” a cewar wani Tunde Ayankoya a Twitter.

Wani Chris Ngonadi yace:

Tunda ba a rufeshi ba, mai zai hana yayi ta surutai. Ba laifin shi bane wannan shirmen da yake yi.

Amma duk da haka, akwai wadanda suke goyon bayan IBB inda suke cewa ta yuwu gaskiya ne.

A cewarsu baya ga rashawa, mulkin Buhari ta janyo ta’addanci mai yawan gaske.

Wani wanda yayi martani mai suna Danielmechi yace:

Babu ta’addanci a lokacin IBB, a lokacin mutanen kirki aka daura don su tafiyar da al’amuran kasa. Kuma cin hanci da rashawa bai yawaita ba.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here