Gwamnatina na ɗaukar Matakai Masu Tsauri ne Don Gina ƙasarmu – Tinubu
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya ce gwamnatinsa na ɗaukar matakai masu tsauri ne domin gina ƙasar tare da samar mata ingantaccen ci gaba.
Yayin da yake jawabi ga ƙungiyar ‘yan asalin Najeriya mazauna China, a birnin Beijing, Shugaba Tinubu ya ce an ƙara farashin man fetur ne a ƙasar, domin samar wa Najeriya ingantaccen ci gaba.
”Za ku ji a ‘yan kwanakin nan ana ta magana game da ƙarin kuɗin man fetur, amma magana ta gaskiya za mu iya gina ƙasarmu? Mu samu tituna masu kyau kamar yadda muka gani a nan (China), mu samu tsayayyiyar wutar lantarki da ruwan sha, kuma kun dai ga yadda makarantunsu ke da kyau a nan”, in ji Tinubu.
Read Also:
Ya ƙara da cewa ”idan muna son cimma waɗannan abubuwa sai mun ɗauki matakai masu tsauri domin samun hanyar da za ta kai mu ga ciyar da ƙasarmu gaba”.
Shugaban ƙasar ya ce ba a samun kowane irin ci gaba cikin sauƙi ko kuma a ɓagas.
“Idan kana son ka samu komai a kyauta, to zai zame maka mai wahalar samu ko ka jima ba ka same shi ba”, in ji shugaban na Najeriya.
”Kalli tituna masu kyau da inganci a nan, ina so na kwaikwayi irin waɗannan ayyuka a Najeriya, ina son gyara makarantun ‘ya’yanmu, bana son ganin ɗalibanmu suna zama a azuzuwan da suka lalace, ina son gayar tsarin koyarwa”, in ji shi.
A ranar Talata ne dai babban kamfanin mai na asar NNPCL ya sanar da ƙarin kuɗin man fetur zuwa naira 855, dangane da inda mutum ke zaune a ƙasar, lamarin da ya ya janyo wa gwamnatin ƙasar suka daga ƙungiyoyi da ɗaiɗaikun mutane