Gwamnati na Daukar Matakan da Suka Dace Domin Ganin an Samu Mafita Game da Matsalar Tsaro – Cif Chukwuemeka Nwajiuba

 

Karamin ministan ilimi ya bayyana dalilin da yasa gwamnati ba za ta tattauna da ‘yan bindiga ba.

A cewar gwamnati, hakan na kara karfafa ‘yan bindiga, kuma suna kara sayen makamai don addabar jama’a.

Ya bayyana cewa, gwamnati na daukar matakan da suka dace domin ganin an samu mafita game da matsalar tsaro.

Karamin Ministan Ilimi, Cif Chukwuemeka Nwajiuba, ya bayyana dalilan da suka sa Gwamnatin Tarayya ta yi watsi da batun tattaunawa da masu garkuwa da dalibai a Najeriya.

Nwajiuba ya yi magana ne ranar Laraba 4 ga watan Agusta yayin amsa tambayoyi daga manema labarai na fadar gwamnati bayan zaman Majalisar zartarwa ta tarayya (FEC) a fadar shugaban kasa, Abuja.

Ya ce ‘yan bindiga suna amfani da kudaden da suka tara daga biyan kudin fansa wajen tayar da kayar baya, wanda hakan ya haifar da rashin tsaro a kasar.

Da yake magana kan abin da gwamnati ke yi kan bidiyon da ya bazu inda wasu masu garkuwa da mutane ke azabtar da wasu daga cikin daliban da aka sace a jahar Kaduna, Nwajiuba ya tabbatar wa ‘yan Najeriya cewa ana kokarin ceto yaran.

Legit Hausa ta tattaro daga Daily Trust, inda ministan ke cewa:

“Gaskiyar magana, abin takaici ne a duk lokacin da aka sace wani dalibin mu a kowane lokaci, ina tabbatar muku da cewa gwamnatin tarayya na yin duk mai yiyuwa.

Mun yi tarurruka da dama tare da jami’an tsaron mu da kuma na wannan yankin baki daya.

Da aka tambaye shi ko akwai matakan da za a bi don ganin makarantun gwamnatin tarayya sun kubuta daga harin ‘yan bindiga, Ministan ya ce:

“Na riga na fada cewa duk hanyoyin ne gwamnati ke bi wajen gudanar da aikin tsaro ba wai kawai a makarantun mu ba.

“Na’am, gwamnatin tarayya ta mallaki wasu kwalejojin tarayya a kewayen Najeriya, daga cikin makarantun sakandare 25,000; Gwamnatin tarayya ta mallaki 120 ne kacal.

Ya ce gwamnati na daukar matakan tabbatar da tsaro a makarantun. “Amma ba mu takaita kanmu ga cibiyoyin mu ba kadai; muna duba tsaro kamar yadda manufar kasa gaba daya aikin gwamnati ne.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here