Za a Dauki Lokaci Kafin a Shawo Kan Matsalolin da Harkokin Sufurin Jiragen Sama a Kasar ke Fuskanta – Hadi Sirika
Ministan harkokin sufurin jiragen sama a Najeriya Hadi Sirika,ya ce za a dauki lokaci kafin a shawo kan matsalolin da harkokin sufurin jiragen sama a kasar ke fuskanta.
Ministan ya yi wannan furunci ne lokacin ganawa da kungiyar masu kamfanonin jiragen sama a Abuja babban birnin kasar.
Read Also:
Ya kara da cewa matsalalolin da bangaren sufurin jiragen sama ke fuskanta a kasar, sun sha kan ma’aikatarsa.
Ya ce wannan ba matsala ce da za a kawo karshenta cikin kankanin lokaci ba, saboda matsala ce ta duniya baki daya, ba Najeriya kadai ba.
Matsalar makamashi matsala ce da ta addabi duniya baki daya. Yanzu haka akwai matsalar tsadar man jirgi a kasashe kama daga Amurka har zuwa New Zealand. Amma matsalar ta fi kamari a Najeriya saboda ba ma sarrafa shi a kasarmu, sannan ga tashin farashin dala” In ji Ministan