Ku Dauki Salon da na Dauka a Gwamnatina Kan Maganin Ta’adin ‘Yan Bindiga – Gwamna Matawell ga Gwamnoni

 

Gwamna Bello Matawalle yana bada shawarar a rungumi yin sulhu da ‘Yan bindiga.

Gwamnan yace hakan ya yi masa amfani wajen kawo zaman lafiya a jahar Zamfara Bello Matawalle ya yi kira ga Gwamnoni su dauki salon da ya dauka a gwamnatinsa.

Zamfara – Bello Matawalle na jahar Zamfara ya ce jahohin Najeriya su dauki matakin sulhu da lalama domin a yaki ‘yan bindiga da sauran matsalolin tsaro.

A ranar Alhamis, 12 ga watan Agusta, 2021, The Cable ta rahoto Gwamna Bello Matawalle yana cewa sulhu da aka yi da ‘yan bindiga ya kawo masu zaman lafiya.

Da yake magana da hukumar dillacin labarai na kasa, gwamnan jahar Zamfara ya bada shawarar ayi koyi da matakin da ya dauka wajen tsare rayuka da dukiyoyi.

Mu gudu tare, mu tsira tare – Matawalle “Kamar yadda na ambata a baya, sha’anin rashin tsaro ba matsalar wasu rukunin mutane kadai ba ce, aikinmu ne mu duka ne.”

“Ko kai jami’in tsaro ne, ko mazaunin gari ko gama-gari, muhimmin abu shi ne, duk mu hadu, mu dauka wannan matsalarmu ce, mu yi kokarin shawo kanta.”

“Bayan na zama gwamnan jahar Zamfara, na san cewa a kwanakin 100 na farko da na yi, mun ci nasarorin da ba a iya samu a shekaru shida da suka wuce ba.”

Yadda Matawalle ya yi a jahar Zamfara

“Mun cin ma wannan nasara ne saboda na kira kowa, na zauna da shi. Mun tattauna da masu ruwa da tsaki; ‘yan siyasa, sarakuna, shugabanni da jami’an tsaro.”

“Muka hada karfi da karfe, shiyasa muka kawo maganar ayi zaman sulhu da lalama da ‘yan bindiga, kuma hakan ya kawo mana nasarori sosai a jahar (Zamfara).”

“Kowace jaha tana bukatar ta dauki irin wannan tsari na samar kwanciyar hankali. Idan muka hadu, muka dauki matsaya daya, na yi imani zai yi mana amfani.”

Jahohin yankin Arewa suna fama da ta’adin ‘yan bindiga da suke kashe jama’a da garkuwa da mutane.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here