Yaduwar Corona: Gwamnatin Daular Larabawa ta Dakatar da Shigar ‘Yan Najeriya Kasar ta
Gwamnatin daular larabawa (UAE) ta dakatar da shigar ‘yan Najeriya Dubai ta jiragen sama a matsayin hanyar dakatar da yaduwar COVID-19.
Babban kamfanin jiragen saman Najeriya, Air Peace, wanda yake kai mutane Sharjah-Dubai, ya sanar da fasinjojin da suke Najeriya wannan sakon.
Sai dai bata dakatar da jiragen da suke mayar da ‘yan Najeriya kasarsu ba tukunna, don haka dokar bata hau kan juragen da suke dauko mutane daga Dubai zuwa Legas.
Gwamnatin daular Larabawa (UAE) ta dakatar da shigar da ‘yan Najeriya zuwa Dubai a matsayin hanyar dakatar da yaduwar cutar COVID-19.
Read Also:
Wannan umarnin ya biyo bayan sa’o’i 24 da da jiragen UAE suka sanar da wannan dakatarwar jirage daga Legas zuwa Abuja.
Babban jirgin da yake kai mutane Dubai daga Najeriya, Air Peace, ya sanar da wannan umarnin na UAE ga fasinjoji.
Air Peace ya bayar da hakuri ga fasinjoji akan wannan al’amari, Daily Trust ta wallafa.
“Kamfanin sufurin jiragen sama na Air Peace tana son sanar da mutane cewa gwamnatin UAE ta dakatar da ‘yan Najeriya daga shiga UAE a matsayin dokar hana yaduwar COVID-19.
“Duk da dai bata dakatar da mayar da ‘yan Najeriya daga Dubai zuwa kasarsu ba. Don haka daukar mutane daga Dubai zuwa Najeriya zai cigaba da wanzuwa har sai 28 ga watan Fabrairun 2021,” cewar kamfanin Air Peace.
Dakatar da zirga-zirgar jirage daga kasa zuwa kasa hanya ce ta dakatar da yaduwar cutar.
Yanzu haka an tabbatar da masu COVID-19 da dama kuma mutane guda miliyan 2.3 ne suka rasa rayukansu.