Yayin Zanga-Zanga: An Sanya Dokar Hana Fita a Borno
Gwamnatin jihar Borno da ke arewacin Najeriya ta ayyana dokar hana fita ra awa 24 a faɗin jihar.
A cikin wata sanarwa, wadda ta samu sa hannun mai magana da yawun rundunar ƴansandan Najeriya a jihar, ASP Nahum Kenneth, ta ce an ɗauki matakin hakan ne domin tabbatar da tsaro bisa ga la’akari da halin da ake ciki.
Sanarwar ta ce: “A ƙoƙarin tabbatar da doka da oda, gwamnan jihar Borno, Babagana Umara Zulum, bayan ganawa da shugabannin hukumomin tsaro a jihar, ya ga wajibcin ayyana dokar hana fita ta awa 24 wadda za ta fara aiki nan take.”
Read Also:
Sanarwar ta ƙara da cewa “an ga buƙatar hakan ne ta hanyar la’akari da fashewar da aka samu wadda ta yi sanadiyyar mutuwar mutum 16 da raunata wasu da dama a jihar.”
Wannan dai na zuwa ne a rana ta farko bayan fara zanga-zangar da matasa suka shirya domin nuna fushi kan matsin rayuwa a ƙasar.
Matasa sun fito a biranen faɗin ƙasar a safiyar Alhamis, inda suke ɗauke da alluna waɗanda ke ɗauke da ƙorafe-ƙorafensu masu nasaba da matsin rayuwa da rashin tsaro.
Sai dai an samu rahotanni na tashin hatsaniya a wasu jihohin ƙasar, inda rahotanni suka bayyana cewa an harbi kimanin mutum uku a jihar Kano, yayin da aka jefa wa masu zanga-zanga barkono mai sa hawaye a yankuna da dama, har da Abuja, babban birnin ƙasar.
A jihar Borno ma lamarin ya so ya dagule a lokacin da aka samu hargitsi a unguwar Bulunkutu, inda jami’an ƴansanda suka jefa barkono mai sa hawaye kan masu zanga-zanga.