Dokar Zaman Gida: A Karon Farko an bi Umarnin IPOB a Abia
Manyan tituna sun zama wayam, sannan shaguna da ma’aikatun gwamnati sun kasance a rufe a fadin Umuahia babban birnin jahar Abia da ke kudancin Najeriya, sakamakon kullen da kungiyar ‘yan awaren Biafra ta IPOB ta saka.
Ko a baya IPOB ta saka irin wannan doka ta zama a gida, da ya hada da rufe makarantu da kasuwanni amma ba ta yi tasiri ba.
Read Also:
A Litinin din da ta gabata mazauna birnin Umuahia sun ce mambobin IPOB sun rika yawo da bindigogi kan tituna, suna hantarar mutane su shige gidajensu.
To sai dai mazauna babban birnin jahar ta Abia sun sami kansu cikin tsaka mai wuya, bayan da gwamnatin jahar ta yi gargaɗin cewa duk ma’aikacin da bai fito aiki ba zai fuskanci hukunci.
To amma bayanai daga jaridar Daily Trust sun nuna cewa kashi 80 basu fita aiki ba a yau Litinin.