Jami’an Tsaro Sun Kashe Mahara 10 a Kaduna

 

Jami’an tsaron Najeriya sun kashe ‘yan bindiga 10 a kusa da Fatika da ke karamar hukumar Giwa da ke jahar Kaduna.

Hakama rahotanni sun ce wasu maharan sun jikkata a musayar wuta da jami’an tsaron.

Kwamishinan tsaro da harkokin cikin gida na jahar Kaduna Samuel Aruwan ya ce jami’an tsaron sun yi nasarar kubutar da wani Alhaji Abubakar Usman da aka yi garkuwa da shi.

Aruwan ya kara da cewa ‘yan bindigar da suka tsere sun bar mashunan su da wata babbar bindiga da wayoyi da fitilu da kuma layu.

Ya kuma shaida cewa an kona wasu daga cikin wuraren da suke ajiye wadanda suka yi garkuwa da su.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here