MDD za ta Fara Aikin Rigakafin Cutar Shan Inna a Afghanistan

 

A karon farko cikin shekaru masu yawa, Majalisar Dinkin Duniya ta ce za ta fara aikin rigakafin cutar shan inna a fadin kasar a Afghanistan.

UNICEF ta ce suna da cikakken goyon bayan shugabannin Taliban kan aikin wanda zai fara a farkon watan Nuwamba.

Hukumar ta UNICEF ta ce kungiyar Taliban ta kuma kuduri aniyar ba da damar sanya ma’aikatan mata cikin kamfen da kuma samar da tsaro ga kungiyoyin.

A baya ‘yan Taliban sun yi adawa da kamfen na allurar rigakafin zargin cewa yana daga cikin wata makarkashiya da kasashen yamma ke yi don hana Musulmai haifuwa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here