Hukumar Lafiya ta Duniya ta Gargadi Kasashen Duniya Kan su yi Hattara da Magungunan Tari na Yara

 

Najeriya ta gargadi ‘yan kasarta da su guji yin amfani da wasu nau’ukan magungunan tari wadanda ake alakanta su da sanadin mutuwar mutane da dama a Gambia.

Ana zargin cewa magungunan iri hudu, na kamfanin hada magani na Maiden Pharmaceuticals da ke Indiya, sun gurbata ne da wasu abubuwa masu cutarwa.

Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ta gargadi kasashen duniya kan su yi hattara da magungunan na yara.

Yanzu haka hukumar kula da ingancin abinci da mugunguna ta Najeriya (NAFDAC) ta bukaci al’ummar kasar da su kaurace wa magungunan.

A cikin wata sanarwa da ta fitar, NAFDAC ta ce duk wanda ya san ya yi amfani da wani daga cikin irin wadannan magunguna, kuma ya ji wasu alamomi da bai gane ba a tare da shi, to ya garzaya ya sanar da hukumomin lafiya.

Hukumar ta kara da cewa wasu daga cikin cututtukan da magungunan ke haifarwa sun hada da ciwon ciki, da amai, da gudawa, da gaza yin fitsari, da ciwon kai, da lalurar koda mai tsanani wadda ka iya sanadin mutuwa.

Sai dai sanarwar ba ta fayyace ko akwai magungunan a kasuwannin Najeriya ba.

Magungunan tarin dai su ne na ‘Promethazine Oral Solution’, da ‘Kofexmalin Baby Cough Syrup’, da ‘Makoff Baby Cough Syrup’ da kuma ‘Magrip N Cold Syrup’.

A wata sanarwa da kamfanin magungunan ya fitar, ta ce ya yi takaicin matsalolin da magungunan suka haifar. Kamfanin ya kara da cewa ya bi duk wasu ka’idojin da aka gindaya na hada magani a kasar Indiya, kuma yana bayar da hadin kai a binciken da ake gudanarwa.

Tuni dai Gambia ta fara janye magungunan daga kasuwanninta.

Ana alakanta magungunan tarin da yin sanadin mutuwar akalla yara 69.

Kuma hukumar lafiya ta nuna fargabar cewa ba a Gambia kawai ake amfani da magungunan ba.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here