Ecowas ta yi Allah Wadai da Garkuwa da Yara 80 a Arewacin Najeriya
Kungiyar Tattalin Arzikin ƙasashen Afirka ta yamma ECOWAS ta yi Allah wadai da garkuwa da yara 80 a arewacin Najeriya cikin makon da ya gabata.
Mafi yawan waɗanda aka yi garkuwa da su a jihar zamfara da ke arewa maso yammcin ƙasar, mata ne da yara waɗanda suka je sharar gona da yin itace a daji.
Read Also:
A wata sanarwa ECOWAS ta yi kira da a saki yaran. Kawo yanzu dai babu wanda ya ɗauki alhakin sace yaran.
Harin dai shi ne na baya-bayan nan a jihar , wadda ke fama da yawaitar hare-haren ‘yan bindiga masu sace mutane domin neman kuɗin fansa.
A makon da ya gabata ma fiye da mutum 70 aka kashe a wasu tagwayen hare-hare a jihar Benue da ke tsakiyar ƙasar.
A ranar Juma’a kuma wasu ‘yan bindigar suka kashe gwamman ‘yan gudun hijira bayan da suka kai wa sansaninsu hari.