Hukumar EFCC ta Cafke Babban Akanta Janar na ƙasar Ahmed Idris
Hukumar Yaƙi da Masu Yiwa Tattalin Arzikin Kasa Ta’annati a Nijeriya EFCC, ta cafke Babban Akanta Janar na ƙasar Ahmed Idris bisa zargin karkatar da kudade gami da almundahanar Naira Biliyan 80.
Read Also:
Wannan na cikin wata takardar sanarwa da hukumar ta aikowa PRNigeria mai dauke da kwanan watan 16 ga watan Mayun 2022, da kuma sa hannun jagoran sashin yada labaran hukumar Wilson Uwujaren, wadda ke tabbata da damke babban akantan.
Wata majiyar sirri daga hukumar ta shaidawa PRNigeria cewa akantan ya kushi kudaden ne ta hanyar wata haramtacciyar hanya tare da yin amfani da ‘yan uwa da abokan arzikida nufin zuba jari a jihar Kano da kuma babban birnin tarayya Abuja.
Sanarwar ta kara da cewa hukumar ta kama shine sakamakon kin amsa gayyatar da ta yi masa, bisa zarge zargen al’mundahana.