Hukumar EFCC ta Gurfanar da Emefiele a Gaban Kotun Tarayya da ke Abuja
Hukumar yaƙi da cin-hanci da rashawa ta Najeriya ta gurfanar da Godwin Emefiele, tsohon gwamnan babban bankin ƙasar a gaban babbar kotun tarayya da ke Abuja a yau Laraba.
Wannan matakin dai ya zo ne bayan umarnin da kotu ta bayar na gurfanar da Emefiele ranar Litinin da ta gabata, ko kuma a sake shi ba tare da wani sharaɗi ba.
Read Also:
Dangane da rashin biyayyar da hukumar ta yi, kotun ta sake nanata umarninta tare da ɗage ci gaba da shari’ar har zuwa ranar Laraba.
Mai shari’a, Olukayode Adeniyi na babbar kotun birnin tarayya ya ba da umarnin a sake Emefiele, wanda ya kwashe sama da kwanaki 149 a hannun jami’an tsaro ba tare da wani sharaɗi ba ko kuma a kai shi kotu domin neman beli.
Ya bayyana a gaban kotu da misalin karfe 12:30 tare da rakiyar jami’an hukumar EFCC.