An Harbe Mai Shekaru 43 a Wajen Gwajin Maganin Bindiga

 

An harbe wani mutum a jihar Bauchi da ke arewa maso gabashin Najeriya wajen gwajin maganin bindiga, kamar yadda kakakin ƴan sanda, Ahmed Wakil ya bayyana.

Ya ƙara da cewa an kama bokan wanda ake zargin shi ne ya bai wa mutumin maganin bindigar sannan kuma ya harbe shi, tare da wasu mutane biyu yayin da sauran waɗanda ake zargi suka gudu.

Kakakin ƴan sandan ya bayyana cewa sunan wanda aka harba shi ne Muhammadu Ali, mai shekara 43.

Kakakin ya kara da cewa, ‘yan sanda sun garzaya wurin da lamarin ya faru, inda suka kai Ali asibiti, sai dai an tabbatar da mutuwar sa a lokacin da suka isa.

Ya kuma gargadi jama’a da su guje wa irin waɗannan abubuwa.

Za a gurfanar da waɗanda ake zargin a gaban kotu bayan an kammala bincike, in ji Wakil.

Ƴan Najeriya da dama sun yi amanna da amfani da asiri wanda suke ganin zai ba su kariya, inda mutane da dama ke tuntubar bokaye kan irin waɗannan batutuwa.

Sai dai an samu rahotannin kashe mutane da dama wajen irin wannan gwaji na maganin bindiga.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com