EFCC ta Kama Hadimin Gwamnan Bauchi
Jami’an EFCC sun cika hannu da wani babban jigon jam’iyyar PDP a Bauchi.
Ana zarginsa da aikata laifin ba cin hanci da rashawa yayi zabe.
An mika shi ga yan sanda kuma sun yi awon gaba shi Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa watau EFCC ta damke Abdon Dalla, babban mai baiwa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed, shawara kan harkokin kwadago.
An damke Abdon Dalla ne da makudan kudade ana zargin yana sayen kuri’u.
Jami’an sun yi awon gaba da Dalla ne ranar Asabar yayin zaben maye gibin kujerar majalisar dokokin mazabar Dass.
Read Also:
An ruwaito Jami’an EFCC sun damkeshi da kudi N1.5m cikin motarsa, kuma aka mikashi ga yan sanda domin bincike.
Shugaban karamar hukumar Dass. Suleiman Mohammed, ya bayyanawa manema labarai cewa kudin da aka kama a hannunsa na ma’aikatan zaben jam’iyyar PDP ne ba nashi ba.
Shugaban, ya ce an damke Dalla ne kawai bayan ya yi jawabi ga yan jarida bayan zabe. “Na samu labarin an damke daya daga cikin mutanenmu kuma na zo domin taya shi jaje.
Ban yi magana da shi ba amma na samu labarin cewa an damkeshi ne bayan jawabin da ya yiwa yan jaridar,” Jaridar Guardian ta ruwaito shugaban da cewa.
“Kudin ba nashi bane, kudin ma’aikatan zaben jam’iyyarmu ne.”