Zamfara: ‘Yan Ta’adda Sun Tashi Gurin Zaben Maye Gurbi

 

Ana dab da fara zaben maye gurbi a karamar hukumar Bakura, ‘yan Ta’adda sun tarwatsa jama’a.

Wurin 8:30 na safe, ‘yan ta’addan sun bayyana daga dajin da ke kusa inda suka kai wa jama’a hari.

Babu kakkautawa jami’an tsaro suka shawo kan ala’amarin sannan jama’a suka dawo.

Wasu mutane dauke da makamai da ake zargin ‘yan bindiga ne sun tarwatsa masu kada kuri’a a kauyen Oroji da ke gundumar Rini ta karamar hukumar Bakura da ke jihar Zamfara a ranar Asabar.

Lamarin ya faru a ranar Asabar yayin da ake zaben maye gurbi na majalisar dattawa, kamar yadda rahoto daga HumAngle ya bayyana.

Jaridar Daily Trust ta bayyana yadda wani mai kada kuri’a mai suna Sulaiman Muhammad, yake sanar da cewa lamarin ya faru wurin karfe 8:30 na safe yayin da ake dab da fara saka kuri’u.

“Ma’aikatan zaben na isowa aka fara shirin saka kuri’u amma sai ga wasu ‘yan bindiga daga daji sun bayyana sannan suka tarwatsa wurin,” Muhammad yace.

“Daga jami’an hukumar har masu saka kuri’u sun tsere amma jami’an tsaro sun bi ta kan ‘yan bindigar,” yace.

A rumfar zabe mai lamba 008, Shiyyar Galadima da ke kauyen Rini, jami’an tsaron sun dinga harbi a cikin iska domin dawo da zaman lafiya bayan ‘yan bindigan sun tarwatsa jama’a.

Hakazalika, rikici ya barke bayan da kwamishinan kananan hukumomi da al’amuran masarautu, Alhaji Yahaya Gora, tsohon kwamishina Alahji Muttaka Rini da kuma mataimakiyar shugaban jam’iyyar PDP, hajiya A’i Maradun sun isa rumfar zabe.

Bayan jami’an tsaron sun fatattaki ‘yan bindigan, an cigaba da zabe kamar yadda rahotanni suka nuna.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here