Hukumar EFCC ta Kama Ma’aikatan Banki Guda 2 Kan Cinye Kudin Mamaci a Jahar Cross River
Hukumar EFCC ta yi nasarar daure wasu ma’aikatan banki da suka cinye kudin mamaci a bankinsu.
Wannan ya faru ne a jahar Cross River a gaban wani alkalin kotu na jahar a jiya Laraba 4 ga watan Agusta.
An yanke musu hukuncin da ya dace dasu, sannan an basu damar biyan beli idan suna da hali .
Read Also:
Cross River – Hukumar EFCC, na yankin Uyo, ta tabbatar da hukunta wasu jami’an bankin guda biyu, Daniel Akpan Eno da Mbuk Idongesit, a gaban mai shari’a Edem Ita Kufre na babbar kotun jahar Cross River, Calabar saboda hadin baki da satar kudi a asusun wani abokin cinikinsu da ya mutu.
An yanke wa mutanen biyun hukuncin ne a ranar Laraba 4 ga Agusta, 2021 bayan sun amsa laifin da ke da alaka da hadin baki na aikata laifi da zamba, Daily Nigerian ta ruwaito.
Wanda ake tuhuma na uku, kuma wanda ake zargi da hannu a barnar, Victor John Okon ba a kama shi da laifi ba. An daga shari’arsa zuwa ranar 10 ga watan Agusta, 2021 domin duba bukatar ba da belinsa.
Mai shari’a Kufre ya yanke hukunci ga Mista Akpan hukuncin daurin watanni ku tare da zabin biyan tarar Naira dubu hamsin (N50,000.00), yayin da aka yanke wa Mista Idongesit hukuncin daurin watanni uku tare da zabin biyan tarar Naira dubu talatin (N30,000.00).