Damfarar N3.bn: Hukumar EFCC ta Kama Tsohon Minista, Ugwuh da Shugaban Kamfanin Ebony Agro

Tsohon minista a Najeriya ya shiga hannun hukumar EFCC bisa zargin hannu a damfarar rancen kudi N3.6bn.

Hukumar EFCC ta kama Charles Chukwuemeka Ugwuh da shugaban kamfanin Ebony Agro Industries Ltd a Owerri jihar Imo.

Mai magana da yawun EFCC ya bayyana cewa za a gurfanar da su a gabam ƙuliya da zaran an kammala bincike kan zargin da ake musu.

FCT Abuja – Hukumar yaki da masu yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa, (EFCC) ta cafke tsohon ministan kasuwanci da masana’antu, Charles Chukwuemeka Ugwuh.

EFCC mai yaƙi da masu rashawa a Najeriya ta damƙe tsohon ministan ne bisa zarginsa da hada baki da k]ma damfarar rancen kudi kimanin Naira biliyan 3.6.

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da mai magana da yawun hukumar yaƙi da cin hanci EFCC, Dele Oyewale, ya fitar kuma hukumar ta wallafa a X watau Twitter.

Sanarwan ta ce an kama tsohon ministan ne tare da Cif Geoffrey Ekenma a ranar 11 ga Janairu, 2024, a lamba 2, Musa Yar Adua Way, New Owerri, jihar Imo.

Meyasa EFCC ta kama tsohon ministan?

Hukumar ta ce an kama mutun biyun ne biyo bayan, “ƙorafin da wani banki ya kai EFCC kan zamba da ake zargin wani kamfani mai suna Ebony Agro Industries Ltd. mai alaka da tsohon ministan.”

Sanarwan ta ce:

“Bincike ya nuna Ugwuh da Ekenma, Manajan darakta na kamfanin Ebony Agro Industries Ltd., sun karɓi bashi daga bankin domin saye da samar da shinkafa.”

“Amma waɗanda ake zargin, a cewar mai shigar da korafin, sun kasa cika hakki da sharaɗin da ya dace a bankin, kuma duk kokarin da aka yi na ganin sun biya bashin kudin ya ci tura.”

Daga karshe, kakakin EFCC ya bayyana cewa hukumar za ta gurfanar da waɗanda ake zargin da zaran an kammala bincike da tattara hujjoji.

 

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com