Jerin Sunayen Kamfanoni 7 da za su yi Dillancin Mai a Matatar Dangote

Yayin da matatar mai ta Dangote ta soma aiki a Najeriya, manyan ‘yan kasuwar mai sun yi rijista don fara dillancin man matatar.

Ya zuwa yanzu dai manyan kamfanoni bakwai ne suka yi wannan rijista, kuma sun kammala duk wata yarjejeniya da matatar.

Haka zalika, dillalan mai masu zaman kansu a Najeriya su ma za su yi zama a wannan makon don cimma matsaya da matatar mai ta Dangote.

Manyan ‘yan kasuwa bakwai a Najeriya sun yi rajista da matatar mai ta Dangote don dillancin man fetur da matatar za ta rinka fitarwa.

Dillalan wadanda ke karkashin kungiyar manyan dillalan man fetur ta Najeriya, a ranar Lahadi sun bayyana cewa da zaran sun kammala sa hannu kan yarjejeniyar za su fara dillancin man.

Jerin sunayen kamfanoni 7 da za su yi dillancin man Dangote

Wannnan na zuwa ne bayan da kungiyar dillalan mai masu zaman kansu suka sanar da cewa a makon nan ne za su gama tattaunawa da matatar mai ta Dangote don fara safarar man.

Jerin manyan ‘yan kasuwa bakwai da za su siyar da man Dangote kamar yadda The Nation ta ruwaito.

1. 11 Plc.

2. Conoil Plc.

3. Ardova Plc.

4. Mrs Oil Nigeria Plc.

5. OVH Energy Marketing Limited

6. Total Nigeria Plc.

7. NNPC Retail

Matatar man Dangote ta fara aiki a Najeriya

A ranar Juma’a 12 ga watan Janairu, Legit Hausa ta ruwaito maku cewa matatar man Dangote ta fara tace mai.

A makon da ya gabata jirgi na biyar dauke da danyen mai samfurin Bonny Light ya sauke kayan a matatar Dangote daga kamfanin mai na masa (NNPC).

Ana sa ran matatar mai ta Dangote za ta rinka tace danyen mai daga nahiyoyi uku da suka hada da Afrika, Amurka da Asia, wanda kuma ake saka ran zai kawo karshen matsalar mai a Najeriya.

Dangote ya fadi wanda ya karfafa masa guiwar bude matatar mai

Jim kadan bayan fara aikin matatar, attajirin Najeriya Aliko Dangote wanda kuma shi ne shugaban rukunin Dangote ya ce Shugaba Tinubu ne ya karfafa guiwarsa har ya bude matatar mai.

Dangote ya nuna jin dadinsa kan yadda shugaban kasa ya ba shi goyon baya, shawarwari da karfafa masa guiwa tun daga farko har zuwa kammala matatar da fara aikin ta.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com