Damfarar N935m: EFCC Tana Neman Matashi Mai Shekaru 24
Hukumar EFCC ta bayyana cewa tana neman wani Adewale Daniel Jayeoba ido ruwa-a-jallo.
Tana neman sa ne sakamakon damfarar N935m da ya tafka tare da hadin guiwar iyayen sa.
Tun watan Yuni iyayen sa suka zo hannun hukumar, amma an neme shi sama ko kasa an rasa.
Jahar Osun – Hukumar yaki da rashawa da harkokin yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta na neman wani Adewale Joyeoba, wanda yake aiki karkashin Wales Kingdom Capital Limited, bisa zargin sa da tafka damfara.
Kamar yadda The Cable ta rawaito, hukumar ta bayyana sanarwar ne a ranar Litinin.
Sanarwar da hukumar ta fitar ya ce:
“Ana sanar da jama’a cewa hukumar EFCC ta na neman Adewale Daniel Jayeoba na Wales Kingdom Capital sakamakon zargin sa da hannu a wata damfara.
“Jayeoba dan shekara 24 ne kuma dan asalin karamar hukumar Ori-Ade ne da ke karkashin jahar Osun.”
Read Also:
“Adireshin sa da aka sani na karshe shi ne 1004, Providence Centre, titin MKO Abiola kusa da gidan man NNPC a Abeokuta, jahar Ogun.”
A watan Yuni, EFCC ta ce jami’an ta daga ofishin ta na jahar Legas su ka kama Emmanuel da Victoria Jayeoba, wadanda su ne iyayen yaron mai shekaru 24 da ake nema bisa zargin su da damfarar naira miliyan 935.
Kamar yadda EFCC ta bayyana:
“Wadanda aka kama sun hada kai ne da dan su wanda har yanzu ake neman sa yana aiki da wani Ponzi Scheme ne da sunan ya na kasuwanci inda yake yasar kudaden al’umma.”
The Cable ta kara rawaito yadda bincike ya gano cewa Emmanuel wanda shi ne darektan Wales Kingdom Capital inda ya ke aiki da asusun bankuna 5 kuma ya shigar da N18,397,913.67 kafin a kama shi.
“Da aka tsananta bincike, an gano cewa Victoria wacce ta bude asusun bankuna 6 ta yashi kudin jama’a har N916,607,715.48.”
Hukumar EFCC ta bukaci duk wanda ya samu labari akan matashin ya yi gaggawar sanar da ko wanne ofishin ta dake fadin kasar nan.