Kudaden da Gwamnati ke Biyan Sanatoci ya Musu Kadan – Rochas Okorocha

 

Rochas Okorocha ya bayyana bukatar gwamnati ta kara kudaden da take biyan sanatoci.

Ya bayyana cewa, kudaden da ake basu sun yi kasa da irin aikin da suke tafkawa a kasar.

Ya kuma bukaci gwamnati da ta rage kudaden da ta ke kashewa na gudanar da gwamnati.

Abuja- Tsohon gwamnan Imo, Rochas Okorocha ya ce kusan Naira miliyan 13 da kowanne sanata ke samu a matsayin albashi da alawus-alawus bai kai wahalar aikin da ‘yan majalisar ta dattawa ke yi ba.

Rochas wanda shi ma dan majalisar dattawa ne ya yi magana ne a wani taron manema labarai a ranar Litinin 20 ga watan Satumba a Abuja, in ji rahoton The News.

Tsohon gwamnan na Imo wanda ke gardama kan ya kamata a rage yawan sanatoci da aka zaba daga kowace jaha zuwa uku ya ce albashin sanata ya kai kimanin naira miliyan biyu tare da alawus na gida na naira miliyan uku da sauran alawus na kusan miliyan 11.

A cewarsa:

“Amma, hakan bai isa ba saboda idan muna da sanata, ya kamata mu biya shi da kyau domin yin aikin da gaske saboda ba shi da wani aiki sai dai kuma idan muna son a yi aikin na dan lokaci ne.”

Ya kamata a rage kudin gudanar da mulki

A bangare guda, ya jaddada bukatar rage kudaden gudanar da mulki a Najeriya da nufin habaka kudi ga kasar.

“Ku tuna, na fadi ya kamata a samu sanata daya a kowace jiha amma hakan ya tayar da cece-kuce a kasar baki daya.

“Amma, jim kadan bayan na yi magana game da hakan Italiya ta rage adadin sanatocinta da kashi 60 cikin dari kamar dai sun ji daga gare ni.

“Kun san Najeriya za ta so a ci gaba da bin tsohuwar hanya, amma idan kuka ci gaba da yin abubuwa kamar yadda kuka saba za ku ci gaba da samun tsohon sakamako, don haka dole ne mu gwada sabon abu.

“Yanzu, da kuke magana game da rage kudaden gudanar da mulki, Najeriya za ta fi kyau a ce tana da sanata daya a kowace jiha da kuma membobin majalisar tarayya uku a kowace jiha. Wannan adadin mutanen na iya magance matsalolin tsarin mulkin Najeriya.”

Son hada kan Najeriya na saka ni hauka, Okorocha ya nuna damuwarsa kan Najeriya

Rochas Okorocha, sanata mai wakiltar Imo ta yamma kuma tsohon gwamnan jahar ta Imo, ya ce hangen nesan sa na hada kan Najeriya yana saka shi ya ji kamar zai hauka.

Okorocha ya yi wannan magana ne a ranar Litinin 20 ga watan Satumba yayin wata tattaunawa da manema labarai da kungiyar ‘yan jaridan Najeriya (NUJ) reshen babban birnin tarayya (FCT). FCT NUJ ta karbi bakuncin tsohon gwamnan na jahar Imo ne gabanin shirin murnar cikarsa shekaru 59 a duniya, The Cable ta rawaito.

Da yake amsa tambaya kan ko zai tsaya takarar shugaban kasa a 2023, Sanatan ya ce:

“Ba ni da burin zama shugaban kasa amma hangen nesa na samun hadin kan Najeriya na haukata ni.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here