Hukumar EFCC ta Rufe Ginin Rabi’u Kwankwaso a Jahar Kano
Hukumar EFCC ta rufe wasu dukiyoyi mallakar Sanata Rabiu Kwankwaso a jahar Kano.
An tattaro cewa matakin da hukumar ta dauka ya biyo bayan korafi da ta samu daga iyalan Ismaila Gwarzo, tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro.
Majiya ya nuna cewa Kwankwaso ya shiga lamarin ne saboda shi ya siya daga cikin kadarorin.
Kano – Hukumar da ke yaki da cin hanci da rashawa (EFCC) ta rufe wasu dukiyoyi mallakar Sanata Rabiu Kwankwaso a jahar Kano, jaridar Daily Trust ta rawaito.
Tsohon gwamnan da a mulki Kano sau biyu, Kwankwaso ya wakilci yankin Kano ta Tsakiya a zauren majalisar dokokin tarayya tsakanin 2011 zuwa 2015.
Read Also:
Jaridar ta kuma rawaito cewa a lokacin da ta ziyarci yankin, daya daga cikin wadanda ke kusa lokacin da jami’an EFCC suka zo don rufe ginin ya yi tsokaci.
Ya bayyana cewa jami’an sun shaida musu cewa rufewar ya biyo bayan wata takardar korafi da hukumar ta samu daga iyalan Ismaila Gwarzo, tsohon mai ba da shawara kan harkokin tsaro.
Majiyar ta ce:
“Batun rufe gidan ya kasance lamari ne na kashin kansa tsakanin ‘yan gidan Ismaila Gwarzo kuma Kwankwaso ya shiga cikin lamarin ne saboda shi ya siya daya daga cikin kadarorin.”
Zuwa yanzu dai ba a ci ta bakin hukumar yaki da rashawar ba kan wannan sabon lamari.
Jaridar Daily Trust ta rawaito a baya cewa hukumar yaki da cin hanci da rashawar na binciken tsohon gwamnan bisa zargin karkatar da kudaden kananan hukumomi da suka kai biliyan N3.08.
Mai magana da yawun hukumar ta EFCC, Wilson Uwujaren, ya tabbatar wa jaridar cewa hukumar na binciken zarge -zargen da ke cikin takardar korafi.