EFCC ta Sako Tsohon Gwamnan Jahar Abia, Sanata Theodore Orji
EFCC ta sako tsohon gwamnan jahar Abia kuma sanata mai wakilyar Abia ta tsakiya, Sanata Orji.
Dama a ranar Alhamis 19 ga watan Augusta hukumar ta kama shi a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja.
Hukumar ta bayyana cewa an baiwa sanatan umarnin bayyana a ofishinta a ranar Juma’a, 20 ga watan Augusta don amsa wasu tambayoyi.
FCT, Abuja – An sako tsohon gwmanan jahar Abia, Sanata Theodore Orji bayan kwashe wasu sa’o’i a ofishin EFCC.
Gidan talabijin din Channels sun ruwaito yadda jami’an hukumar EFCC sun damki sanatan a filin jirgin Nnamdi Azikwe dake Abuja a ranar Alhamis, 19 ga watan Augusta.
Read Also:
Hukumar EFCC ta sako tsohon gwamnan bayan ya sha tambayoyi a kan harkokin kudaden da yayi tsakanin 2007 da 2015 inda ake zargin rashawa.
EFCC ta ce shekarar da ta gabata Sanata Orji ya bayyana gabanta yana bukatar su sakar masa wasu takardu da za su bashi damar fita Dubai don duba lafiyarsa.
Hukumar ta kula da yadda sanatan ya ki mayar da takardun bayan ya dawo daga tafiyar tasa.
Don haka hukumar ta bukaci Orji ya dawo hedkwatarta a ranar Juma’a don ya cigaba da amsa tambayoyi.
Sai dai sanatan ya musanta rike shi da aka yi. A cewarsa jami’an EFCC tsare shi kawai suka yi a hanyarsa ta zuwa London don duba lafiyarsa.
Premium times ta rawaito yadda gwamnan ya sha tambayoyi tare da dansa Chinedu, kakakin majalisar jahar Abia wanda ya bayyana a ofishin bayan ya ji EFCC ta kama mahaifinsa.