Gwamna El-Rufa’i da Gwamna Lalong Zasu Hada Kai Don Magance Matsalolin Tsaro

 

Gwamnan jahar Kaduna ya yi alkawarin hada kai da na jahar Filato don magance matsalolin tsaro.

Ya bayyana haka ne yayin da ya kai ziyarar jajantawa a jahar ta Filato biyo bayan kashe-kashe da suka faru.

Gwamnan ya ce, jahar Kaduna da ta Filato jahohi ne masu kamanceceniya ta fuskoki da yawa.

Plateau – Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, da takwaransa na jahar Filato, Simon Bako Lalong, sun yi alkawarin hada kai da rundunar Operation Safe Haven (OPSH) da sauran hukumomin tsaro don magance matsalolin tsaro da ke addabar jahohin biyu.

Sun yi wannan alkawari ne ranar Lahadi 5 ga watan Satumba lokacin da El-Rufai ya ziyarci Lalong don jajantawa gwamnati da mutanen jahar Filato kan hare-hare da kashe-kashen da aka yi a wasu sassan jahar, Daily Trust ta rawaito.

Gwamna El-Rufai ya ce:

“Filato da Kaduna ba makwabta ne kawai ba. Muna da dangantaka mai karfi kuma tun lokacin da muka hau mulki a 2015, ni da Gwamna Lalong muna tuntubar juna; Gwamna Lalong ne ya gabatar da mu ga Cibiyar Tattaunawar Ba da Agaji, wata kungiya mai zaman kanta ta duniya da ke aikin wanzar da zaman lafiya.

“Gwamna Lalong ne ya gabatar da ra’ayin cewa ya kamata jahohin biyu su kafa hukumomin gina wanzar da zaman lafiya.

“Filato tana da Hukumar Wanzar da Zaman Lafiya kuma Kaduna tana da Kwamitin Zaman Lafiya, muna aiki tare domin mun fahimci cewa jihohin mu biyu suna da girma kuma gidaje ne ga mutane da yawa a fadin Najeriya.

“Har sai idan mun inganta zaman lafiya tsakanin mutane daban-daban, sabanin haka rikici ba zai shafi jahohin biyu kadai ba har ma da kasar baki daya. Dangane da rikicin baya-bayan nan tsakanin Irigwe da Fulani, muna da Irigwe a Karamar Hukumar Kaura a Jahar Kaduna.

“Muna kuma da Ganawuri da Atakar a sassan Kudancin Jahar Kaduna, mu mutane daya ne kuma dole ne mu hada kai mu hada kan mutanen mu don mu zauna lafiya”.

Lalong, wanda ya samu wakilcin Mataimakinsa, Farfesa Sonni Tyoden, ya ce hada kai tsakanin jahohin biyu zai dakile barazanar tsaro da ke fuskantar su.

Lalong ya jinjina wa El-Rufa’i bisa zuwansa don jajantawa gwamnati da al’ummar jahar Filato kan rikice-rikicen da ke faruwa a jahar.

A bayanansa:

“Gaskiya ne Filato da Kaduna ba makwabta ne kawai ba, alabashshi suna da tarihi na dogon lokaci, don haka abin da ya shafi Filato ya shafi Kaduna kuma abin da ya shafi Kaduna ya shafi Filato.

“A wannan lokacin bakin ciki, zai saukaka lamurra lokacin da abokai masu tunani iri daya suka zo don magance matsalarsu. Muna godiya da nuna kawancen ku, muna godiya da tausayawar ku.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here