Sarkin Borgu ya Roki Shugaba Buhari da a Turo Dakarun Sojoji Yankin Masarautarsa
Sarkin Borgu, Muhammad Dantoro, ya roki shugaba Buhari ya bada umarnin a tura dakarun sojoji yankin masarautar Burgu.
Wannan kiran na zuwa ne bayan wasu yan bindiga sun sace basaraken Wawa dake yankin masarautar Burgu.
Sarkin ya kuma bayyana cewa yana nan cikin koshin lafiya kuma rahoton dake cewa an sace shi ba gaskiya bane.
Niger – Sarkin Borgu, jahar Neja, Muhammad Dantoro, ya yi kira ga shugaban ƙasa, Muhammadu Buhari, ya taimaka ya bada umarnin a turo sojoji yankin Burgu domin magance masu garkuwa, kamar yadda punch ta rawaito.
Da yake martani kan sace Basaraken Wawa, Dakta Mahmud Ahmed, wanda aka yi a Burgu, Sarkin yace ya zama wajibi akansa ya yi wannan kiran ga shugaban ƙasa.
Sarkin yace:
Read Also:
“Wannan kiran na gaggawa ne, muna bukatar gwamnati ta gaggauta turo mana dakarun sojojin ƙasa da na sama domin su binciko mana yan tada kayar baya.”
Sarki ya musanta rahoton sace shi
Basaraken ya musanta raɗe-raɗen cewa yan bindiga sun sace shi, inda ya kara da cewa yana nan cikin koshin lafiya.
“Mutane na kusa da na nesa sun kira ni ta wayar salula, suna son tabbatar da lafiya ta. Eh ina lafiya, ba ni maharan suka sace ba, hakimin Wawa aka ɗauke kuma a karkashin masarautata yake.”
“Hakanan kuma, an sace basaraken Dekara watanni huɗu da suka gabata kuma har yanzun ba’a gano shi ba.”
“Bana jin daɗin abinda ke faruwa a yankina, kuma ina rokon a turo sojoji su shiga dajin Kainji domin su kuɓutar da basaraken da sauran mutanen da yan bindiga ke tsare da su.”
Sarkin Borgu yace ya kamata a gaggauta ɗaukar mataki tun kafin maharan su fice daga dajin zuwa jamhuriyar Benin.