El-Rufa’i ya yi Martani Akan Rashin Tsaron Jaharsa

Gwamna El-Rufai na jihar Kaduna ya bayyana damuwarsa a kan rashin tsaron da ke addabar jaharsa.

A cewarsa, ‘yan sandan da yakamata a ce suna yakar ‘yan ta’adda suna can suna rike jakunkunan manyan mata.

Ya bayyana bukatarsa ta canja kundin tsarin Najeriya domin bai wa jihohi damar amfana da ‘yan sandansu.

Gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya nuna takaicinsa a kan yawan ‘yan sandan da ya kamata su yi yaki da ta’addanci amma suna can suna yin akasin hakan, kamar rikewa matan manyan mutane jakunkuna.

El-Rufai ya ce ya harzuka a kan kashe-kashen da ake yi a jiharsa, ya kuma bayyana bukatar ‘yan sanda su shiga lamarin.

Ya bukaci majalisar tarayya da ta gyara dokar bai wa jihohi damar amfana da ‘yan sanda da kansu.

Gwamnan ya ce ya kamata a ce gwamnonin jihohi ne suke da alhakin kulawa da ayyukan yau da kullum na ‘yan sandan jahohinsu.

El-Rufai ya yi maganar ne a ranar Litinin da daddare a gidan talabijin din Channels, shirin da The Punch suka kula dashi.

A cewarsa, “Mun dade muna cece-kuce a kan yadda ya kamata a ce an baiwa jihohi damar amfana da ‘yan sandansu.

“Sannan yawan ‘yan sandan da muke da su a Najeriya ba za su wadacemu ba, ba su wuce rabin yadda muke bukata ba.

Sannan a hakan da yawansu suna can suna ayyukan da ba za su amfani al’umma ba, kamar rike jakunkunan matan manyan mutane.

“Ya kamata a ce muna da ‘yan sanda da yawa a Najeriya, hakan zai samu ne idan aka yi gaggawar canja kundin tsarin mulki kuma kwamitin kishin kasa na APC ya bukaci ‘yan sanda, wannan zai bayar da damar kara yawan ‘yan sanda.

“Idan aka bai wa jihohi damar amfana da ‘yan sandansu, gwamnatin tarayya za ta dinga biyansu albashi, amma gwamnatin jaha za ta iya biyan ‘yan kudaden mai na motocinsu da sauransu.

“To me muke tsoro? Mu yi gaggawar gyara kundin tsarin mulkin don gwamnatin jahohi ta fara samun damar amfana da ‘yan sandan ta.”

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here