Sabuwar Zanga-Zanga: Ba Zamu Lamunta ba – IGP ga Matasa

Sifeta janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu ya ja kunnen matasan da ke shirin rikito wata zanga-zangar EndSARS.

Ya ce sam ba za su lamunci tayar da zaune tsaye ba, za su dauki tsauraran matakai a kan duk wanda ya aikata hakan.

Ya fadi hakan ne bayan jin labarin matasa suna shirin ballo wata zanga-zangar a ranar 5 ga watan Disamba.

Gwamnatin tarayya za ta taka wa duk wani mai zanga-zanga a kan cutarwar dan sanda da wasu matsololi makamantan haka burki, jaridar Thisday ta wallafa haka.

Ta ce duk wanda ya gwada kawo cikas ga zaman lafiya ko kuma harkar tsaron kasa zai kwashi kashinsa a hannu.

Gwamnatin tarayya ta zargi za a fara wani sabon zanga-zanga na EndSARS a ranar 5 ga watan Disamba, wanda yake ta yawo a kafafen sada zumuntar zamani.

Sifeta janar na ‘yan sanda, Mohammed Adamu ya sanar da hakan bayan ya yi taro da kwamishinonin ‘yan sandan jihohi 36 da ke fadin kasarnan a ranar Juma’a, inda yace wajibi ne jami’an tsaro su yi wa al’amarin garanbawul.

Kamar yadda matasa suka yi zanga-zanga a watan Oktoba, wanda matasan kudu da na Abuja suka rikitar da kasar gabadaya.

Al’amarin ya janyo tashin hankula iri-iri, har rikicin kashe-kashen Lekki Tollgate da aka yi ranar 20 ga watan.

Rikicin ya yi sanadiyyar mutuwar ‘yan sanda 22 sannan har dukiyoyin gwamnati da na al’umma matasan suka lalata na tiriliyoyin nairori.

 

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here