Kamfanin Zirga-Zirgar Jiragen Sama na Emirates ya Sake Soke Jigilar Shiga da Fita Daga Najeriya

Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na Emirates mallakar Daular Larabwa ya sake soke jigilar shiga da fita daga Najeriya har zuwa 30 ga watan Nuwamba.

Cikin wata sanarwa da ya wallafa, kamfanin ya ce kwastomomin da suka je ko suka bi ta Najeriya cikin kwana 14 da suka wuce ba za a bari su shiga jirginsa ba da zai je Dubai.

“An soke dukkan tikitin da aka saya,” a cewar sanarwar da ya wallafa a shafinsa. An sake dakatar da sufurin ne kwana biyu kacal bayan kamfanin ya sanar da ci gaba da jigilar bayan shafe makonni da dakatarwar.

A watan Maris Emirates ya sanar da dakatar da zirga-zirga zuwa ƙasar yayin da ake ci gaba da sa–in-sa tsakanin gwamnatin Najeriya da Daular Larabawa game da gwajin cutar corona.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here