kwana 25 da Rufewa: An Buɗe Layukan Intanet a Sudan

Hukumomi a Sudan sun buɗe layukan intanet kusan wata ɗaya da rufe su biyo bayan juyin mulkin da sojoji suka yi wanda ya hamɓarar da gwamnatin riƙon ƙwarya.

An dawo wa da dukkan kamfanonin sadarwa sabis ɗinsu na intanet a ranar Alhamis.

A ranar 9 ga watan Nuwamba ne kotu ta umarci kamfanonin da su buɗe layukan amma toshewar ba su yi hakan ba.

Shafin Netblocks mai lura da ayyukan intanet ya tabbatar da dawo da sabis ɗin.

“An dawo da layukan intanet a Sudan a kwana na 25 bayan toshe su; bayanai sun nuna cewa an samu ƙaruwa a sabis ɗin waya daga ƙarfe 4:30 na yammacin ƙasar; babu tabbas ko sabis ɗin zai ci gaba da zama ko kuma har zuwa yaushe,” a cewar Netblocks.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here