EndSARS: Ana Shirin Fara Sabuwar Zanga-Zangar
Akwai fargabar cewa ana shirin fara sabuwar zanga-zangar EndSARS bayan CBN ya sami yardar kotu don daskarar da asusun wasu masu zanga-zanga.
Kotun ta ba CBN izinin daskarar da asusun har zuwa lokacin da za ta kammala bincikenta.
Tuni lamarin ya kawo tsaiko a harkokin kwamitin shari’a na Lagas yayinda umurnin kotun ya shafi daya daga cikin wakilan matasa da ke kwamitin Wani rahoto daga jaridar The Nation ya nuna cewa akwai barazana na fara sabuwar zanga-zangar #EndSARS wanda bata gari suka kwace a baya.
A cewar rahoton, sabon ci gaban zai kasance ne sakamakon daskarar da asusun wasu shahararrun matasa da suka gudanar da zanga-zangar #EndSARS da aka yi.
Read Also:
An tattaro cewa Babban Bankin Najeriya (CBN) ya sami umurnin kotu don daskarar da asusun mutane da kungiyoyi 20 wadanda ke da nasaba da zanga-zangar ta #EndSARS.
Umurnin kotun ya shafi daya daga cikin wakilan matasa a kwamitin shari’a ta Lagas, Rinu Oduala.
Hakan, ya yi sanadiyar dage zaman kwamitin yayinda wakilan matasan suka kauracewa zaman a ranar Asabar, 7 ga watan Nuwamba.
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa yan Najeriya da dama musamman matasa sun je shafukan soshiyal midiya domin yin Allah-wadai da yunkurin babban bankin kasar, cewa hakan na iya haifar da sabuwar zanga-zanga.
An tattaro cewa kotun ta umurci bankuna da su daskarar da dukkanin harkoki a asusun bankunan masu zanga-zangar na #EndSARS da abun ya shafa har na tsawon kwanaki 180 zuwa lokacin da za a samu sakamakon binciken da CBN ke gudanarwa a yanzu.
A gefe guda, kwamitin bincike kan barnar da aka yi wa rundunar yan sandan Najeriya a yayin zanga-zangar neman a rushe rundunar tsaro na SARS, ya bayyana cewa an sace bindigogin AK-47 kimanin guda 100 a Lagas.