Najeriya: Shugaban Kasar ya Dakatar da Babban Daraktan Hukumar Nazari da Bincike

 

Tun kafin ya hau mulki Buhari ya ke ikirarin cewa zai yaki cin hanci da rashawa.

A lokacin da ya ke yakin neman zabe, Buhari ya taba cewa; “idan Najeriya ba ta kashe cin hanci ba, cin hanci zai kashe Najeriya”.

Sai da, jama’a da dama sun zargi gwamnatin Buhari da yin amfani da hukumomi domin matsawa ‘yan adawa da sunan yaki da cin hanci Shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya amince da dakatar da Charles Agulanna, babban daraktan hukumar bunƙasa tsare-tsare (PRODA) bisa zarginsa da rashawa.

Sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, shine ya fidda sanarwar a wata takarda da yasa hannu kuma ya aika ta zuwa ofishin ministan kimiyya da fasaha, Ogbonnaya Onu.

Takardar mai lamba SGF.6/S.19/T/211 na ɗauke da kwanan watan 5 ga watan Nuwamba.

A cewar takardar, an umarci Dani Onjeh, shugaban gudanarwa na hukumar da shima ya ajiye muƙaminsa. Boss Mustapha ya ce darakta mafi girman matsayi da yake hukumar zai cigaba da jagorantar hukumar har sai ofishinsa ya kammala bincike.

“Na rubuta don cika umarnin bisa yarjewarsa kamar haka; “dakatar da Injiniya Dr C.N Agulanna babban daraktan hukumar bunƙasa tsare-tsare (PRODA) da ke Enugu, har zuwa lokacin da za’a kammala bincike”, a cewar takardar.

Sannan aka kara da cewa; “an gaggauta sauke Kwamared Daniel Onjeh, shugaban gudanarwa na hukumar PRODA har sai an kammala bincike.”

Ana zargin Ogulanna da rarraba kwangila ba bisa ka’ida ba, barin aiki ba tare da izini ba, fitsara da rashin kunya, alfarma, aiki da kuɗi ta hanyar da basu dace ba, da kuma watsi da tsare-tsaren hukuma.

Sauran laifukan da ake zarginsa sun haɗar da ,wasarere da muhimman bayanai, aikata ɓarna, karɓar kuɗi ta hanyar barazana gami da tilasta ma’aikata da ƴan kwangila.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here