Enugu: Rayyuka da Dama Sun Salwanta Yayin da Trela ta yi Karo da Motar Bus
Mummunan hatsari da ya faru a jihar Enugu ya yi sanadin rasuwar mutum 21 ciki har da yara ‘yan makaranta.
Hukumar kiyayye haddura, FRSC, ta tabbatar da afkuwar hatsarin inda ta ce trela ce ta kubce ta fada wa motar daukan ‘yan makarantar – Kwamandan hukumar FRSC na jihar Ogbonna Kalu ya ce tukin ganganci da gudu fiye da ka’ida ne sanadin afkuwar hatsarin Hukumar Kiyayye Haddura ta Kasa, FRSC, a ranar Alhamis ta tabbatar da rasuwar mutane 21 ciki har da yara ‘yan makaranta sakamakon hatsarin mota a Mgbowo a karamar hukumar Awgu ta jihar Enugu.
Read Also:
Kwamandan rundunar ta Enugu, Mista Ogbonna Kalu wadda ya tabbatar wa The Punch afkuwar lamarin a wayar tarho ya ce hatsarin ya faru ne a ranar Laraba da rana,
Ya ce trela ce da motar bas ta kai yara makaranta hatsarin ya ritsa da su. Kwamandan ya ce gudu fiye da ka’ida ce dalilin afkuwar hatsarin da kuma tukin ganganci.
Kalu ya ce,”An tabbatar da mutuwar mutum 21 kuma fiye da mutane 50 ke cikin bas din. “Kazalika, ba yara ‘yan makaranta ne kadai suka mutu ba. Wadanda ke sana’a a gefen titi suma suna daga cikin wadanda suka rasu.”Daga bayanin da muka samu, tukin ganganci ne ya janyo afkuwar hatsarin.”
Amma majiyar Legit.ng ta tattaro cewa abin bakin cikin ya faru ne a lokacin da trelar mallakar wani kamfanin gine-gine da ke aiki a Rafin Oji a Awgu ya kubce ya fada wa motar bus na ‘yan makaranta dauke da yara fiye da 60 ‘yan Presentation Nursery and Primary School, Awgu