Zamfara: An yi Batakashi Tsakanin Sojoji da ‘Yan Bindiga

 

Har yanzu ba a daina samun rahotannin cewa ‘yan bindiga sun kai hari ba a jihar Zamfara.

A ranar Laraba ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya bayyana cewa sun shawo kan matsalar tsaro a yankin arewa maso yamma – Rundunar soji da ta ‘yan sanda sun kaddamar da atisaye daban-daban domin kawo karshen ‘yan bindiga a jihohin Katsina, Sokoto, da Zamfara.

A ranar Alhamis ne wasu ‘yan ta’adda da ake zargin ‘yan bindiga ne suka yi musayar wuta da dakarun rundunar soji a kauyen Gidan Goga da ke yankin karamar hukumar Maradun a jihar Zamfara, kamar yadda Daily Trust ta rawaito.

Daily Trust ta rawaito cewa wasu ‘yan bindiga sun kai hari Gidan Goga a kan babura da misalin karfe 1:00 na ranar Alhamis.

Mazauna kauyen sun sanar da Daliy Trust cewa ‘yan bindigar sun budewa jama’a wuta bayan shigarsu kauyen kafin daga bisani su yi awon gaba da shanu da sauran dabbobin da ake kiwo a gida.

Wani tsohon kwamishinan ilimi a jihar Zamfara, Alhaji Ibrahim Danmalikin Gidan Goga, ya tabbatarwa da Daily Trust cewa ‘yan bindiga sun kai hari kauyen da misalin karfe daya na rana. “An sanar da sojoji kuma sun yi sa’ar zuwa sun tarar da ‘yan bindigar kafin su gudu.

“An yi musayar wuta tsakanin sojoji da ‘yan bindigar, ba zan iya cewa ga adadin mutanen da suka mutu ba, amma na san cewa mutane da yawa sun bar gidajensu,” a cewarsa. Kafin wallafa wannan rahoto, Daily Trust ba ta samu kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara, SP Muhammad Shehu, a waya ba domin jin ta bakinsa a kan kai harin.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here