Fadar Shugaban Kasa Tayi Rashin Babban Ma’aikaci
Fadar shugaban kasa ta fada alhini da makokin rasuwar Babatunde Lawal sakamakon ciwon kansa.
Lawal mai shekaru 56 ya rasu a ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba, bayan shekaru biyu da nada shi babban sakatare.
A sakon ta’aziyyar sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha ya kwatanta mutuwar Lawal da ikon Allah Babatunde Lawal, babban sakataren a ofishin sakataren gwamnatin tarayya, Boss Mustapha, ya rasu.
Lawal ya rasu a ranar Juma’a, 6 ga watan Nuwamba bayan fama da cutar kansar hanta da yayi.
Read Also:
Ya rasu bayan daukar shekaru biyu da yayi a kan mukaminsa. Masani ne a fannin tattalin arziki tare da tsari.
Ya fara aiki da gwamnatin tarayya a watan Oktoban 1987 a matsayin jami’in tsari a ma’aikatar tsari da tattali ta tarayya.
Mamacin ya yi aiki a wurare da dama wadanda suka hada da mamba a kwamitin asusun tarayya da kuma kudin shiga kuma yayi aiki da NBS.
A daya bangaren, SGF Mustapha ya nuna damuwarsa tare da alhininsa a kan mutuwar Lawal, ya kwatanta rasuwarsa da ikon Allah.
A wata takarda da babban sakataren ofishin SGF ya fitar, Maurice Nnamdi Mbaeri, Mustapha ya ce ya matukar damuwa da mutuwar Lawal.