A kori Ma’aikata ‘Yan Faransa – Malaman Addini ga Gwamnatin Kano

Malaman addinin jihar Kano sun bukaci Gwamna Abdullahi Ganduje ya yi gaggawar dakatar da ‘yan kasar Faransa daga yi wa jihar aiki.

Hakan ya biyo bayan sukar musulunci da shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron yayi, wanda hakan ya harzukar da musulman duniya.

Kungiyar ta isar da wannan sakon nata ne a wata takarda, wacce sakataren kungiyar, Dr Saidu Dukawa, ya saka hannu Daukacin malaman addinin jihar Kano da ma’aikatu masu zaman kansu sun yi kira ga Ganduje a kan ya cire duk wani dan kasar Faransa daga yin ayyuka a jiharsa.

Wannan ya biyo bayan sukar musulunci da Emmanuel Macron yayi, wanda hakan ya fusatar da musulman duniya.

Idan ba a manta ba, shugaban kasar Faransa, Macron, ya harzukar da musulman duniya, bayan ya bayyana niyyarsa ta yakar musulunci, sannan ya kwatanta imani da musulunci a matsayin lamarin da yake raba kawunan jama’a. Wannan al’amarin ya hassala musulman da ke fadin duniya.

Kungiyar Musulmai ta Kano, ta sanar da hakan a wata takarda da sakatarensu, Dr Saidu Dukawa, ya saka hannu.

Sun yi kira ga gwamnatin da tayi gaggawar musanya yaren Faransa da na Larabci a tsarin makarantun gwamnatin jihar.

Kungiyar ta hada da malamai masu karantar da litattafan addini da kuma na jami’a.

Sun ce yin hakan ne kadai zai kawo kwanciyar hankali da zaman lafiya, shafin Linda Ikeji ya wallafa.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here