Jama’a A Cigaba da Addu’a – Zulum

Gwamnan jihar Borno, Babagana Zulum, ya jinjina wa kotun Dubai a kan yankewa mutane 6 masu daukar nauyin Boko Haram hukunci.

An gano yadda suka yi ta tura wa ‘yan Boko Haram kusan naira miliyan 300, ta hanyar canja kudin daga dala zuwa naira a karo na 17.

Dama a watan Fabrairu da Oktoba, gwamnan ya roki mutanen jiharsa da su yi azumin kwana 2 don Allah ya tona wa masu daukar nauyin Boko Haram asiri Gwamnan jihar Borno, Farfesa Babagana Zulum ya jinjina wa kotun Dubai, a kan yanke wa mutane 6 masu daukar nauyin ‘yan Boko Haram hukunci, Daily Trust ta wallafa.

Ya yi farin cikin yadda cikin shekaru 11, aka samu hanyar gano masu daukar nauyin ‘yan Boko Haram, wanda kungiyar ta yi ajalin dubbannin mutane da kuma rasa gidajen miliyoyin mutane, har da ma’aikatan gwamnatin wadanda suka kai kimar dala biliyan 9 a jihar Borno da sauran wuraren arewa maso gabas da Najeriya gabadaya.

Sakon Zulum, wanda ya bayar a wata takarda ranar Talata, wacce kakakinsa, Malam Isa Gusau ya bayyana, ya bayar da labarin ya yadda kotun Abu Dhabi ta yanke wa wasu mutane 6 hukunci a kan tura wa kungiyar Boko Haram kusan Naira miliyan 300.

Wadanda aka yankewa hukuncin, kamar yadda ta tabbatar, sun tura dala 782,000 zuwa asusun Boko Haram a karo na 17, daga Dubai zuwa Najeriya, tsakanin 2015 zuwa 2016.

Dama gwamnan ya roki al’ummar jiharsa da su yi azumi a watan Fabrairu da Oktoban wannan shekarar, na kwana biyu, don addu’ar samun sauki a kan musibar Boko Haram.

Kuma ya roki ‘yan jihar da su yi addu’ar Allah ya fallasa asirin duk wadanda suke daukar nauyin kungiyar.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here