Fadar Shugaban Kasa ta Kare Ministan Sadarwa, Dr. Isa Pantami

 

Ministan sadarwa da tattalin arziki na zamani, Isa Pantami, ya sha suka kan maganganun da yayi wadanda ke cike da rudani.

‘Yan Najeriya sun yi kira ga ministan da ya yi murabus daga mukaminsa ko kuma gwamnatin tarayya ta tsige shi.

Sai dai kuma fadar shugaban kasa ta kare Pantami, tana mai cewa wadanda ke neman a tsige shi ne ke ingiza kiraye-kirayen murabus din sa.

Daga karshe fadar shugaban kasar Najeriya ta mayar da martani game da zargin cewa ministan sadarwa da tattalin arzikin zamani, Dr. Isa Pantami, ya yi kalamai a baya yana mai goyon bayan kungiyoyin ‘yan ta’adda.

anin fadar shugaban kasar na kunshe ne a cikin jerin sakwannin da babban mai taimakawa shugaban kasa na musamman kan harkokin yada labarai da yada labarai, Malam Garba Shehu ya fitar a Twitter.

Shehu a cikin jawabin nasa a ranar Alhamis, 22 ga Afrilu, ya kare ministan tare da gabatar da cewa Pantami ya ce akwai kuruciya tare da shi a lokacin da yayi wadannan kalaman.

A cewar kakakin shugaban kasar, a halin yanzu Pantami na fuskantar tirjiya wanda wasu da ke neman a tsige shi daga matsayin minista suka ingiza.

Ya ci gaba da cewa lokaci ya wuce, kuma tunannin ministan ya canza.

Ya ce abun bakin ciki ne yadda a yau ake yiwa shugabannin siyasa da na addini da na kungiyoyin fararen hula shagube dangane da kalamun da suka yi a baya koda sun yi watsi da su.

Har ila yau ya ce irin hakan kan shafi rayuwa da harkokin irin wadannan mutane ba tare da la’akari da lokacin da suka yi su ba.

Yayin da take nuna goyon bayansa ga ministan da ke cikin rudani, fadar shugaban kasa ta bayyana nasarorin da Pantami ya samu a wannan gwamnati mai ci.

Ya ce:

“A yau, akwai wani sabon salon yiwa shugabannin siyasa da na addini da na kungiyoyin fararen hula shagube dangane da kalamun da suka yi a baya – komai dadewa, har ma bayan sun yi watsi da su.

“Irin wannan lamarin kan shafi rayuwa da harkokin wadannan mutane kan abunda suka fadi, ba tare da la’akari da lokacin da suka yi su ba.

“Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki na zamani,@DrIsaPantami yana fuskantar irin wannan kamfen din a halin yanzu, inda masu neman a cire shi daga mukaminsa suke zuga lamarin.

“Ba su damu da abin da ya fadi ko bai faɗi ba shekaru 20 da suka gabata:

wannan shine kawai makamin da suke amfani da shi don ganin a raba shi da mukaminsa.

Amma za su ci riba idan aka dakatar da shi daga yanke shawara da zai inganta rayuwar ‘yan Najeriya na yau da kullun.

“Ministan ya nemi gafara game da abin da ya fada a farkon 2000.

Ba a yarda da ra’ayoyin ba a lokacin, kuma ba zai zama abun yarda ba a yau, idan da zai maimaita su. “Amma ba zai sake maimaita su ba – don ya fito fili ya yi tir da maganganun da ya yi a baya a matsayin kuskure.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here