Fafatawa Tsakanin ‘Yan Bindiga da Sojoji
Rahotanni sun bayyana cewa an shafe tsawon dare ana barin wuta a tsakanin sojoji da ‘yan bindiga a tsakanin Zaria zuwa Kaduna.
‘Yan bindiga sun matsa wajen yawaita kai hare-hare a yankin Zaria da kewaye a ‘yan kwanakin baya bayan nan.
An shafe tsawon dare guda ana gumurzu tsakani jami’an sojoji da ƴan bindiga akan titin Zaria zuwa Kaduna.
Mun samu rahotannin cewa an shafe daren ranar Lahadi zuwa wayewar garin ranar Litinin ana ta faman bata kashi tsakanin sojoji da ƴan ta’adda daga titin Zariya zuwa Kaduna daf da garin Jaji, a cewar BBC Hausa.
Read Also:
Kwamishinan tsaron cikin gida na jihar Kaduna, Samuel Aruwan, shine ya tabbatarwa da BBC afkuwar lamarin yayin wata ganawa, inda ya bayyana cewa al’amarin ya faru a kusa da garin Jaji.
Ya ce sun tura jami’an tsaron don daƙile maharan daga aikita ta’addanci bayan sun sami rahotannin sun kai hari.
Wani maƙwabcin yankin ya ce tun a daren Lahadi, ƴan fashin suka tare hanyar tsakanin Jaji da kwanar Faraƙwai, kana suka tare hanyar da ke tsakanin Lamban Zango da Dumbi-Dutse.
Kwamishinan tsaron bai bayar da gamsassun muhimman bayanai dangane da ba-ta-kashin da aka yi.
Al’ummar yankin sun shaidawa BBC cewa ƴan bindigar sun kashe mutane biyu a wata motar alfarma ƙirar Luxurious, sannan jami’an tsaro sun sheƙe biyu daga cikin ƴan bindigar.
Kana ɓarayin sun jikkata mutane da dama baya ga ƙwamushe wasu da yin garkuwa da su.
Sai dai wasu majiyoyi na cewa jami’an tsaro sun yi nasarar kuɓutar da waɗanda aka yi garkuwar da su.