Jahar Kaduna ta Fara Aikin Naira Biliyan Goma na Gina Wurin kiwo ga Makiyaya – Gwamna El-Rufa’i

 

Gwamnan jahar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce jaharsa za ta kammala wurin kiwon shanu nan da shekaru 2.

Gwamnan ya sanar da cewa babban bankin Najeriya ne ya taimaka da N7.5 biliyan daga cikin N10 da aikin zai lamushe.

Malam Nasiru El-Rufai ya ce matsalar makiyaya za ta kau kuma hakan zai zama babbar hanyar kiwon dabbobi.

Abuja – Gwamna Nasir El-Rufai na jahar Kaduna a ranar Talata, ya ce jaharsa ta fara aikin naira biliyan goma na gina wurin kiwo ga makiyaya a jahar Kaduna.

Daily Trust ta rawaito cewa, El-Rufai, wanda ya zanta da manema labarai yayin wani taro da jami’an jam’iyyar APC a sakateriya jam’iyyyar da ke Abuja, ya ce nan da shekaru biyu za a kammala aikin.

Gwamnan ya ce babban bankin Najeriya na CBN shi ya taimaka wa jahar da kudi har N7.5 biliyan domin samun nasarar aikin, Daily Trust ta rawaito.

Ya ce kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya tuni suka dauka matsayarsu kan kiwo a sarari inda suka ce ba hanya ba ce mai bullewa a bangaren kiwon dabbobi.

“Amma kuma yin wurin kiwo ba a dare daya bane. Dole ne mu kasance masu tsari, dole ne mu kasance da shiri kuma mu tabbatar zai iya aiki. Mun dauki matsayarmu a matsayinmu na gwamnoni kuma za mu tabbatar ya yi aiki.

“A jaha ta a misali, muna kokarin samar da wurin kiwo ga makiyaya. Kuma wannan ne kadai hanyar shawo kan matsalolin. Amma kuma za a iya yin shi a dare daya?

“Wannan aikin da muke yi zai kwashi naira biliyan goma. CBN ce ke tallafa mana da naira biliyan bakwai da rabi kuma za mu kwashe shekaru biyu kafin mu kammala.

“Kuma ina fatan Fulani makiyaya su ga wannan a matsayin wata hanyar samar da dabbobi da kiwonsu a maimakon kaiwa da kawowa da su daga gonar wannan zuwa ta wani. Muna son shawo kan matsalar.”

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here