Faransa ta Haramta Sayar da Wayoyin iPhone 12 a ƙasarta
Hukumomi a Faransa sun umurci kamfanin Apple da ya daina sayar da wayoyinsa na iPhone 12 a ƙasar, suna iƙirarin tana fitar da tururin radiyeshan (radiation) mai yawa sama da wanda Tarayyar Turai ta amince wayoyi su iya fitarwa.
Read Also:
Hukumar sa ido kan tururin sinadaren radiyeshan na ƙasar ANFR ta sanar da Apple shawarar da ta yanke bayan ta gudanar da gwaje-gwaje.
Kamfanin na Amurka yana da kwanaki goma sha biyar don sabunta manhajarsa wadda hukumomin Faransa suka ce zai rage tururin radiyeshan na wayar zuwa matakan da za a amince da su.
Idan kamfanin Apple bai cika wannan wa’adin ba, gwamnati ta ce za ta dakatar da sayar da dukkan wayoyinsa na iPhone 12 a ƙasar.
Har yanzu dai kamfanin Apple bai mayar da martani ba.