Faransa ta yi Allah wadai da Goyan Bayan Sanya Hijabi a Turai
Gwamnatin Faransa ta yi Allah wadai da wani kamfen da ɓangaren kare haƙƙin ɗan Adam na majalisar Turai ta ƙaddamar a intanet da nufin ƙarfafa amincewa da tsarin sanya hijabi ga mata a Musulunci.
Matakin wanda ya samu goyon bayan ƙungiyar Tarayyar Turai kuma take ɗaukar nauyi – yanzu an janye shi.
Shirin ya ƙunshi fuskokin mata, wasu sanye da mayafi ko hijabi wasu kuma babu.
Taken shirin shi ne: “Ado yana cikin bambance-bambance kamar yadda sanya hijabi ƴanci ne; ya kamata a girmama hijabi.”
Read Also:
Majalisar Turai mai hedikwata a Strasbourg ta ce matakin na cikin shirinta na yaƙi da kyamar musulmi.
Amma a Faransa, ɓangarorin siyasa ne suka mayar da martani.
Ministar matasa a gwamnatin shugaba Macron, Sarah el-Hairy ta ce shirin wani matakin na ƙarfafa sanya hijabi ya saɓa wa aƙidun Faransa.
Eric Zemmour da ke neman takarar shugaban ƙasa da za a yi watan Afrilu mai zuwa, ya faɗi a Twitter cewa: “Musulunci addini ne da ya saɓawa ƴanci, kuma wannan maƙiyin gaskiya ne.”
Saboda adawa da matakin a Faransa, majalisar Turai ta janye kamfen ɗin tana mai cewa za ta bi wasu hanyoyi na isar da saƙon.