ISWAP ta Kashe ‘Yan Sanda 2 da Soja 1 a Malam Fatori 

 

Rahotanni daga jahar Borno na cewa ISWAP ta kashe yan sandan Najeriya biyu da soja daya a wani hari da kungiyar ta kai Malan Fatori.

PRNigeria ta rawaito cewa jami’an tsaro na daga cikin rundunar hadaka da za su tarbi yan gudun hijira da ake shirin dawowa dasu gida.

A wata mai kama da haka rahotanni daga Magumeri duk dai a jahar Bornon na cewa mahara da ake zaton mayakan ISWAP ne sun kai hari a wani asibiti da ke garin.

Kamar yadda jaridar Daily Trust ta rawaito maharan sun buda wuta ne da zuwansu asibitin, sun kuma kona karfen sabis din kamfanin waya na Airtel.

Hakama akwai rahotannin da ke cewa sun kwashi magunguna da sauran kayayyaki.

Wata majiyar tsaro ta ce “maharan sun kasa kansu gida biyu, inda wasu suka rika bata kashi da jami’an tsaro, yayin da daya bangaren ya shiga kwasar kayan asibiti da suka hada da magunguna da firjin da kuma zannuwan gado.”

Karamar hukumar Magumeri na da nisan kilomita 40 ne daga birnin Maiduguri na jahar Borno.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here