Farashin Kuɗin Wutar Lantarki ya ƙaru a Najeriya
Bincike ya nuna cewa farashin kuɗin wutar lantarki ya ƙaru da kashi 58 cikin 100 tun bayan da gwamnatin Najeriya ta janye tallafin naira biliyan 500 da take bai wa fannin samar da lantarki.
Read Also:
Jaridun Najeriya sun rawaito cewa tun shekara ta 2020 aka cire tallafin, al’amarin da ya haifar da karuwar farashin wutar lantarkin daga N31/kWh zuwa N49/kWh tun a bara.
Sannan tun bayan wannan lokaci kuma, an sake samu karin farashin wutar da N18/kWh.
A baya dai kamfanonin rarraba wutar lantarki a kasar sun sanar da bijiro da wani tsari na kasafta wutar rukuni-rukuni da ya kunshi iya kuɗinka iya shagalinka.