Ina Farin Cikin Ganin Irin Nasarorin da Ake Samu a Karkashinka – Shugaba Buhari ga Marwa

 

Nasara bayan nasarar da Janar Buba Marwa (rtd) yake samu a NDLEA ya burge Muhammadu Buhari.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kira shugaban hukumar NDLEA ta wayar salula daga Amurka.

Kakakin shugaban kasa, Femi Adesina ya fitar da jawabi, yana cewa Buhari yana alfahari da aikin Marwa.

Abuja – Shugaba Muhammadu Buhari ya yi jinjina na musamman ga shugaban hukumar NDLEA ta kasa watau Buba Murwa kan irin kokarin da yake yi.

Kamar yadda jaridar The Cable ta kawo rahoto, Muhammadu Buhari ya kira Buba Marwa ta wayar salula domin yabawa abin kwazon da jami’ansa suke yi.

Yabon da shugaban kasa ya yi wa Birgediya Janar Buba Marwa mai ritaya ya zo ne bayan jami’an NDLEA sun yi nasarar karbe tulin hodar iblis a jihar Legas.

Rahotanni sun ce darajar hodar iblis da aka karbe a yankin Ikorodu a Legas ya kai na N194b.

Femi Adesina ya fitar da jawabi

A jawabin da Femi Adesina ya fitar a ranar Litinin, an ji cewa Mai girma shugaban kasa ya kira Janar Marwa yayin da yake halartar taron UN a Amurka.

“Ina mai matukar godewa aikin da ka ke yi wajen magance matsalar miyagun kwayoyi. Ina farin cikin ganin irin nasarorin da ake samu a karkashinka.

“Ka na ta kara nuna ba ayi tumin-dare wajen zabenka da aka yi a matsayin wanda zai jagoranci wannan yaki da masu nema hallaka matasanmu ba.”

“Ka cigaba da namijin kokarin da kake yi.”

– Muhammadu Buhari

Shugaban kasa ya yi murna Leadership take cewa Mista Adesina yace Muhammadu Buhari ya nuna farin cikinsa ga NDLEA a gaban tawagarsa da ke halartar taron majalisar dinkin Duniya.

An ji shugaban kasar yana yabawa shugaban na NDLEA a zamansa da abokan rakiyarsa.

“Buba Marwa yana kokari. Tan biyu na hodar iblis, wannan gagarumin aiki ne.”

– Muhammadu Buhari

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here