‘Yan Sandan Jihar Jigawa Sun Kama Mutane 2 da Ake Zargi da Garkuwa da Mahaifiyar Sanata Abdulkarim Abdulsalam

 

Jigawa – Yan sanda a Jihar Jigawa sun kama mutane biyu da ake zargi da kashe jami’in hukumar shige da fice da kuma garkuwa da mahaifiyar sanatan APC mai wakiltar Kano ta tsakiya, Abdulkarim Abdulsalam.

Kakakin yan sandan jihar, Lawal Adam, ya ce yan sanda da yan bijilante ne suka gano wadanda ake zargin a wurare daban-daban a Kano da Jigawa, rahoton Premium Times.

A watan da ta gabata, Premium Times ta rahoto yadda yan ta’adda suka kashe jami’in shige da fice ɗaya suka raunata wasu biyu a karamar hukumar Birniwa, da ke da iyaka da Jamhuriyar Nijar.

Kazalika, a watan Yuni, yan bindiga sun sace mahaifiyar Mr Abdulsalam a gidanta da ke karamar hukumar Ungogo a Kano.

Daya baya an sako mahaifiyar dan majalisar bayan an biya kudin fansa.

‘Yan sandan sun ce an kama wadanda ake zargin ne a sansanin makiyaya a karamar hukumar Gabasawa na Jihar Kano, da kauyen Laraba Gurgunya a karamar hukumar Taura a Jigawa.

Mr Adam ya ce:

“A ranar 18/09/2022 tsakanin karfe 7 na yamma da 12.15 na rana, bayan samun bayanin sirri, tawagar yan sanda da yan bijilante daga hedkwata a Dutse da Ringim sun yi samame na musamman da ta yi sanadin kama hatsabiban yan ta’adda da ke adabar Jigawa da Kano.

“Yan sandan sun ce binciken farko ya nuna wadanda ake zargin ne suka kashe jami’an shige da fice a ranar 9 ga watan Agusta da kashe yan sanda a kauyen Kwalam a karamar hukumar Taura a ranar 23 ga watan Janairu yayin amsa kirar kai dauki.”

Wadanda ake zargin da aka kama sune Safiyanu Muhammad, 35, mazaunin rugar makiyaya a Gabasawa Jihar Kano, da Musa Idi, 40, na rugar makiyaya ta Laraba Gurgunya, Taura, Jihar Jigawa.

Kwamishinan yan sanda na Jigawa, Bashir Ahmad, ya yaba da kokarin jami’an da yan bijilante bisa aiki mai kyau da suka yi.

Dakaci karin bayani…

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here