Calabar: Wasu Bata Gari Sun Kai Farmaki Ofisoshin NLC, INEC, SEMA da Wasu Hukumomi
Fusatattun matasa da ake zargin ‘yan daba ne tun tafka mummunan ta’asa a wasu hukumomin gwamnati a Calabar.
Hukumomin da matasan suka kai hari sun hada da NLC, INEC, SEMA da kuma wasu kantuna da kasuwannin zamani – Matasan sun kwashi kayan abinci, kayan ofis, tare da lalata abubuwa da dama a wuraren da suka yi kutse ‘Yan daba sun lalata ginin hukumar zabe, INEC, kungiyar kwadago, NLC, da hukumar kiyaye afkuwar hadura (SEMA) inda suka yi awon gaba da kayan abinci, suka kuma lalata dakin ajiyar kayyakin.
Read Also:
Masu zanga zangar sun kuma lalata kadarorin miliyoyin naira a sashen ma’adanan da suka shafi danyen mai, cibiyar tafiye tafiyen kasuwanci, kasuwar zamani ta Value Mart da kuma gidan jaridar “Chronicle” mallakin jihar Cross River. Daily Nigerian ta ruwaito cewa sun tura wakilansu zuwa wajen da abubuwan suka afku, rahotanni sun bayyana cewa akwai kayan abinci, kayyakin ofis irin su inji, na’urar sanyaya daki, kumfutoci, kujeru, dama wasu da dama da aka lalata.
NAN sun rawaito cewa barnar da akayi anyi ne cikin duk da dokar ta bacin da gwamnati ta saka a jahar. Sai dai Gwamna Ben Ayade na Cross River, lokacin da yake bayyanawa a taron wata hira da ya gabatar a gidan talabijin yace zanga zangar #ENDSARS ta dauki wani salo daban a jahar. “Zanga zangar #ENDSARS zanga zanga ce da dukan mu muka shaida bukatunku kuma muna tare da ku a wannan yanayin. Wannan ya bamu dama a matsayin mu na shugabanni mu gane irin fushi, radadi, bacin rai da kuma bujirewa da matasa ka iya yi, ina tare daku a wannan lokacin na tsanani. “Amma yaku yayan jihar nan masu girma, idan muka lalata dukiyoyin mu a matsayin mu na jiha mafi karancin kaso, baza mu samu damar sake dawo dasu ba,” a cewarsa. Gwamnan ya kuma ce ya lura da yadda matasa suka nuna damuwarsu wanda hakan ya sashi gabatar da jawabi.
“Ya ku ‘yan Cross River, yanzu ba lokacin dorawa juna laifi bane, lokaci ne na nuna kulawar da damuwa. “Kowane dan siyasa yana da ýan adawa, amma a wannan lokaci ya kamata muji tsoran Allah mu hada kai mu dawo da farin cikin a lokacin matsin nan. “Muyi kokarin shawo kan wannan matsalar mu samu damar taya juna murnar dawowar farin cikin mu. “Dan Allah mun gane kuskuren mu, ayi hakuri a bamu damar yin gyara. Babu dan adam daya zama gwani. Kuma menene damuwarku, ku bar Cross river haka, a samu zaman lafiya. ” Ina rokonku, dan Allah mu yacewa juna. Mu hada kai mu yaki wanda zasu lalata mana jiha,” a fadar gwamnan.