IGP: Abin ya Isa Haka

 

Sifeto Janar na yan sanda, IGP Mohammed Adamu ya bada umurnin tura jami’an yan sanda domin kawo karshen lalata, sace-sacen da kashe-kashen da ake yi a fadin tarayya.

Ya bada umurnin ne ga dukkan mataimakan Sifeto AIG, Kwamishanoni, kwamandoji da masu yaki da ta’addanci. Kakakin hukumar yan sanda, Frank Mba, ya bayyana hakan a jawabin da ya saki ranar Asabar, a birnin Abuja . Adamu ya umurci manyan jami’an yan sanda su tabbatar da cewa kowa ya shiga taitayinsa. Musamman ya umurci kwamishanoni da shugabannin rundunonu su tura jami’ansu wuraren da suke shugabanta domin tabbatar da zaman lafiya.

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here