Ibadan: An Sace Babura 300 da Wasu Kayayyaki a Gidan Sanata

Wasu matasa da ake zargin ƴan daba ne sun kai hari gidan Sanata Teslim Folarin a Ibadan Matasan sun sace kayayyaki kamar babura da firinji da kuɗin su ya kai naira miliyan 200.

Sanata Folarin ya tabbatar da afkuwar lamarin inda ya ce kayan tallafi ne da zai raba a watan Disamba Wasu da ake zargi ƴan daba ne a ranar Asabar sun kai hari gidan Sanata Teslim Folarin dan jamiyyar APC mai wakiltar Oyo Central da ke Ibadan sun sace kayan tallafi da kuɗin su ya kai N200m. Folarin ya tabbatar da faruwar mummunan lamarin yayin wani shirin gidan rediyo a ranar Asabar a Ibadan kamar yadda Daily Trust ta ruwaito. An gano cewa kayayyakin da aka sace na tallafi ne ga mazabarsa da ɗan majalisar zai yi a watan Disamba.

web design guest post

 
VISIT OUR OTHER WEBSITES
PRNigeria.com EconomicConfidential.com Hausa.PRNigeria.com
EmergencyDigest.com PoliticsDigest.ng TechDigest.ng
HealthDigest.ng SpokesPersonsdigest.com TeensDigest.ng
ArewaAgenda.com Hausa.ArewaAgenda.com YAShuaib.com

LEAVE A REPLY

Please enter your comment!
Please enter your name here